Sojojiun HKI A Kudancin Kasar Lebanon Sun Kashe Mutane Fararen Hula Wasu Kuma Suka Ji Rauni A Yau Lahadi

Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji

Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji rauni a safiyar yau.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana cewa mutanen kudancin kasar Lebanon sun komawa gidajensu da suke kudancin kasar kan iyaka da kasar Falasdinu da aka mamaye ne, sai sojojin yahudawan, suka bude masu wuta suka kashe wannan adadin.

A yau Lahadi ne 26 ga watan Jeneru ne, wa’adin ficewar sojojin HKI daga kasar Lebanon yake cika kamar yadda ya zo cikin yarjeniyar da suka sanyawa hannu da kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata.

Wannan bas hi ne kate hurumin yarjeniyar da aka sanyawa hannu da HKI ba, tun bayana tsagaita wuta sojojin yahudawan suka fara kutsawa cikin wasu yankuna a kasar ta Lebanon. Sun kuma kashe wasu mutanen kasar wadanda suka samu a cikin gidajensu a kan iyakar kasashen biyu, duk da cewa an kulla yarjeniyar zaman lafiya.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa a yau Lahadi ma, sojojin yahudawa sun kama mutane biyu yan kasar Lebanon a garin haula na kudancin kasar. Sannan wani jirgin yaki wadanda ake sarrafashi daga nesa ya yi harbi a wasu yankuna na kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments