Kakakin sojojin kasar ta Yemen Janar Yahya Sari, ya sanar a jiya Asabar cewa, sun kai hari a kan yankin “Umrashrash” da ake kira da Eliat, ta hanyar harba makamai masu linzami samfurin “Ballistic’ mai suna; “Zul-Fikar”.
Sari ya ce hari na farko an kai shi ne, ta hanyar amfani da makami samfurin Ballistic, sai kuma na biyu da makamai mai fika-fikai.
Kakakin sojojin kasar ta Yemen ya kuma ce sun kai harin ne saboda ci gaba da taimakawa al’ummar Gaza da ‘yan gwgawarmayarsu da suke fuskantar kisan kiyashi daga HKI.
Janar Sari ya jaddada matsayin kasar ta Yemen, na ci gaba da kai wa HKI hare-hare har sai an kawo karshen yaki Gaza.
Tun bayan da HKI ta shelanta yaki a kan al’ummar Falasdinu, kasar ta Yemen ta shiga cikin masu taya Falasdinawan yaki, ta hanyar kai wa manufofin HKI hare-hare da jirage marasa matuki, da kuma makamai masu linzami. Haka nan kuma sun hana jiragen ruwa masu bi ta tekun “Red Sea” zuwa tasoshin jiragen ruwan HKI.