Sojojin Yemen Sun Kai Harin Makami Mai Linzami A Kan Filin Jirgin Lud ( Ben Gorrion) Na Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Lod da makami mai linzami nau’in ‘Palestine 2’ Dakarun sojin Yemen sun

Sojojin Yemen sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Lod da makami mai linzami nau’in ‘Palestine 2’

Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani harin soji na musamman da aka kai kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami kirar “Palestine 2”.

A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin jiya, Rundunar Sojin Yemen ta bayyana cewa: Farmakin ya sanya miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya tsere zuwa matsuguni karkashin kasa tare da dakatar da ayyukan tashar jirgin sama.

Sanarwar ta ce harin da aka kaiwa filin jirgin sama na Lod nasara ce ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma mujahidansu, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suka yi a zirin Gaza.

Sanarwar ta yi kira ga daukacin al’ummar Larabawa da na Musulunci da su fito kan tituna “don nuna goyon bayansu ga ‘yan uwansu a Gaza, saboda yadda suke fuskantar zalunci da wuce gona da iri na killacewa.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted