Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman

Sojojin ruwan Iran sun sanar da cewa, wani jirgin ruwan Amurka na yaki da ya yi kokarin shiga tekun Oman, ya fuskanci gargadi daga sojojin ruwan Iran tare da tilasta masa janyewa. Da saiyar yau Laraba ne dai jirgin sama mai saukar angulu mallakin sojojin ruwa, ya yi gargadi ga jirgin ruwan na Amurka da […]
Fiye Da Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da Mutanen Gaza Ke Ciki

Kungiyoyin agaji da kuma na hakkokin bil’adama sun yi gargadi akan yunwar da ake fama da ita a Gaza, tare da yin kira ga gwamnatoci da su yin matsin lamba domin kawo karshe killace Gaza da aka yi, da kuma shigar da kayan agaji a cikin yanki. Kungiyoyin sun kuma dorawa HKI alhakin halin da […]
Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”

Ofishin Fira ministan kasar Iraki ya fitar da bayani a yau Laraba akan abinda ya gudana a tsakanin Muhammad Shiya al-Sudani da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a tattaunawar wayar tarho. Sakataren harkokin wajen Marco Rubio ne ya kira yi fira ministan Iraki inda su ka tattauna alakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma […]
An Kama Wata Mata Da Take Shirin Kashe Benjemin Netanyahu

Kafafen watsa labarun HKI sun ambato hukumar leken asiri ta “Shabak’ tana sanar da kame wata mace, dake zaune a tsakiyar wannan haramtacciyar kasa bayan da aka tuhumeta da Shirin kashe Fira minister Benjamin Netanyahu. ‘Yan sandan HKI sun ce, matar da aka kama ta so yin amfani da abubuwa masu fashewa da ake kerawa […]
A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10. Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111. Wannan adadin yana nuni […]
Iran Ta Jaddada Hakkinta Na Tace Sinadarin Uranium A Cikin Kasarta

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa; Ba zai yiwu Iran ta iya yin watsi da shirinta na inganta sinadarin Uranium ba Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Har yanzu ba a daina sarrafa sinadarin Uranium ba a Iran, duk da irin barnar da hare-haren Amurka ya yi wa cibiyoyin makamashin nukiliyar […]
Babban Hafsan Sojin Iran Ya Ce: Iran Zata Sanya Duk Wanda Ya Dauki Matakin Wuce Gona Kanta Nadama

Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure, za su fuskanci mayar da martani da karfi Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin wani kuskure, to za su fuskanci mayar da martani mai karfi da zai wurga su […]
Sojojin Yemen Sun Kai Harin Makami Mai Linzami A Kan Filin Jirgin Lud ( Ben Gorrion) Na Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Lod da makami mai linzami nau’in ‘Palestine 2’ Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani harin soji na musamman da aka kai kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami kirar “Palestine […]
Yahudawan Sahayoniyya Sun Bullo Da Dabarar Kisa Kan Falasdinawa Musamman ‘Yan Gudun Hijira

Wani sabon salon gwamnatin mamayar Isra’ila na neman kashe Falasdinawa ‘yan gudun hijira da tsananta yunwa kansu Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun rufe tekun ga masunta da ‘yan gudun hijira a zirin Gaza, matakin da ke kara dagula al’ummar Gaza da aka killace. Gabashin tekun kudancin Gaza shi ne mashigar da mazauna yankin da […]
Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi tsohon shugaban kasar Barack Obama da cin amanar kasa tare da yin kira da a yi masa shari’a Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi magabacinsa, Barack Obama da cin amanar kasa, inda ya bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya kan wani rahoton sirri da ya […]
Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Iran Na Nukiliya Ya Yi Kama Da Tabuwa

Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran. Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta […]
Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza

Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka […]
Jami’an Rasha, China, Iran Sun Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa A Tehran

Kasashen Iran, Rasha, da China sun gudanar da wani taro a birnin Tehran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi Shirin Iran na nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakaba mata. Taron kasashen ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin hadin gwiwa da tuntubar juna a cikin lokuta masu zuwa. Kamfanin dillancin […]
Trump ya fitar da Amurka daga UNESCO bayan amincewa da Falasdinu a matsayin Mamba

Amurka ta yanke shawarar ficewa daga hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a karo na biyu saboda matakin da ta dauka na shigar da Falasdinu a matsayin mamba. Mataimakiyar sakatariyar yada labaran fadar White House Anna Kelly ta sanar da matakin a cikin wata sanarwa a ranar Talata. […]
Eritrea ta gargadi Habasha game da yunkurin kafa tashar jiragen ruwa a cikin yankinta

Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa […]