Sojojin Yemen Sun Kai Hari Da Makami Mai Linzami Kan Ma’aikatar Yakin Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari da makami mai linzami kan ma’aikatar yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da ke birnin Jaffa Majiyar rundunar sojin Yemen a safiyar

Sojojin Yemen sun kai hari da makami mai linzami kan ma’aikatar yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da ke birnin Jaffa

Majiyar rundunar sojin Yemen a safiyar yau Talata ta fitar da sanarwar cewa: Dakarun sojin Yemen sun aiwatar da wani gagarumin farmakin soji kan ma’aikatar yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Jaffa da aka mamaye.

Rundunar sojin ta Yemen ta watsa wata sanarwa a ta bakin kakakinta Birgediya Janar Yahya Sari’e a yau Talata cewa: Dakarunta sun harba makami mai linzami kan ma’aikatar yakin gwamnatin yahudawan sahayoniya a yankin Jaffa da aka mamaye da nau’in makami kirar Falastinu 2.

Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: Makamin mai linzamin ya kai ga inda aka saita shi, kuma na’urorin kakkabo makaman yahudawan sahayoniyya sun kasa dakile harin makamin, lamarin da ke nuni da cewa wannan aiki shi ne na uku cikin sa’o’i 12 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted