Sojojin Yemen Da Hadin Gwiwar ‘Yan Gwagwarmayar Iraki Sun Kai Hare-Hare Kan Yankunan ‘Yan Sahayoniyya

Sojojin Yemen da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar Iraki sun kai wani farmaki na hadin gwiwa kan yankunan yahudawan sahayoniyya Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar

Sojojin Yemen da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar Iraki sun kai wani farmaki na hadin gwiwa kan yankunan yahudawan sahayoniyya

Kakakin Rundunar Sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya sanar da cewa: Sun kai wani harin soji na hadin gwiwa da ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki, inda hari ya kai kan wani wuri mai muhimmanci a kudancin Falasdinu da aka mamaye ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki.

Sanarwar ta kara da cewa: Sojojin saman Yemen sun kai farmakin soji guda biyu, na farko sun kai harin ne kan birnin Ashkelon, yayin da na biyu kuma suka kai kan yankin Jaffa da ke karkashin mamayar yahudawan sahayoniyya, a matsayin goyon bayan al’ummar Falasdinu da ake zalunta da kuma goyon bayan ‘yan gwagwarmayar a Zirin Gaza.

Kakakin rundunar sojin kasar ta Yemen ya kuma kara da cewa: An gudanar da ayyukan biyu ne da jirage marasa matuka ciki guda biyu wadanda suka samu nasarar tsallake na’urorin tsaron sararin samaniyyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tare da cimma burinsu cikin nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments