Falasdinawa fiye da 33 ne, suka yi shahada a wani hare-haren kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a
Rahotonni sun bayyana cewa: Tun daga wayewar garin jiya Juma’a ne sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka fara aiwatar da hare-haren kisan kiyashi kan al’ummar Zirin Gaza, inda akasarin wadanda hare-haren suka ritsa da su mata ne da kananan yara da suke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira karkashin tantuna.
Majiyoyin kiwon lafiya sun bayar da rahoton cewa: A yammacin jiya Juma’a adadin shahidai Falasdinawa ya karu zuwa shahidai 33 da suka hada da yara da mata, sakamakon ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a Zirin Gaza.
Kamar yadda majiyoyin suka bayyana cewa: Wani jirgin leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai hari kan gungun Falasdinawa da ke zaune a kan rufin wani gida na iyalan Shahidai a yankin Ard Abu Salim da ke yammacin sansanin Nuseirat a tsakiyar Zirin Gaza, inda ya janyo shahadan Falasdinawa 6 tare da jikkata wasu na daban da aka kai su asibitin Al Awda bayan la’asar a jiyan.