Sojojin Ruwan Isra’ila sun kai farmaki kan jiragen ruwa na Sumud Flotilla

Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki

Kungiyar Global Sumud Flotilla ta fitar da wata sanarwa a daren jiya Laraba inda ta sanar da cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun kai farmaki a kan jiragenta da ke kan hanyar isa Gaza domin kai kayan agaji, inda suka lalata kamarori da kuma sauran kayan ayyukan fasaha da suke cikin wasu daga cikin jiragen Ruwan, sannan kuma suka killace su.

Baya ga haka kuma sun kama dukkanin mutanen da suke cikin wasu jiragen sun tafi da su.

Sanarwar ta ce, kyamarorin da ke cikin jirgin sun samu matsala, sannan sojojin Isra’ila sun shiga jiragen ruwa da dama, inda suka umurci jiragen da su karkata zuwa tashar jiragen ruwa ta Asdod da ke karkashin ikon su.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun ayyana dokar ta baci kan jiragen ruwa, tare da dakile hanyoyin sadarwa da kuma kakkabe kyamarorin sa ido. An rasa hanyoyin  tuntuɓar jiragen ruwa da dama, yayin da aka gano nakiyoyin sojan ruwa guda huɗu a kusa da wurin, kuma an ga jiragen yaƙin Isra’ila fiye da 20 sun kewaye su.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun ruwaito cewa sojojin ruwan kasar sun shiga jiragen ruwa da dama,  inda suka kwace jiragen ruwan Alma da Sirius tare da kame wadanda suke a cikinsu.

Masu fafutuka daga kasashe 44 ne suka shiga cikin wannan tawaga wadda ta hada mutane fiye da 500, da suka hada da ‘yan siyasa da kuma fitattun mutane masu fafutuka a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments