Sojojin Ruwa Na Kasar Iran Sun Karbi Jingin Ruwan Yaki Mafi Girma Kirar Cikin Gida Mai Suna Zagros

A wani labarin kuma a atisayen ‘Iktidar 1403’ wanda sojojin kasar Iran suke gudanarwa, sojojin ruwa sun karbi jirgin ruwan Yaki Mafi girma na zamani

A wani labarin kuma a atisayen ‘Iktidar 1403’ wanda sojojin kasar Iran suke gudanarwa, sojojin ruwa sun karbi jirgin ruwan Yaki Mafi girma na zamani wanda aka gina a cikin ginda wanda aka sanya masa suna Zogros.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatar da bikin kaddamar da jirgin da kuma mika shi ga sojojin ruwa na kasar ne a sansanin sojojin ruwa na Konarak da ke lardin Sistan Baluchistan na kudancin kasar.

Labarin ya kara da cewa babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Burgediya Janar Muhammad Bakiri ne ya jagoranci kaddamar da jirgin ruwan yakin mai suna “Zagros Mai lalatawa’ , wanda yake aiki da kayakin zamani a ayyukansa, har’ila yau wanda yake iya amfani da makamai daban-daban, kama daga masu linzami zuwa makaman igwa.

Babban kwamandan sojojin ruwa Janar Abdolrahim Mousavi, da Rear Admeral Sharan Irani babban kwamandan sojojin ruwa na kasa da wasu jami’an sojojin kasar ne suka sami halattar taron kaddamarwa da kuma mika jirgin ruwa da rundunar sojojin ruwa na kasar.

Labarin ya kara da cewa Zagros zai fara aikinsa a cikin wannan makon da muke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments