Sojojin ruwa na kasar Iran sun fara atisayen soje na kwanaki biyu a kudancin tekun indiya wanda aka sanya masa suna (Karfin mai dorewa na 1404), inda zasu gwada makaman garkuwa na makamai masu linzami da dama saboda kare sararin samaniyar kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa atisayen zai hada abubuwa da dama, wadanda suka hada da makamai masu linzami masu cin dogo, matsakaicin da karamin zango.
Idan an kammala akwai tabbacin iran zata tabbatar da karfinta na kariya daga makamai daban-daban.
Banda haka akwai makamai masu linzami da za’a gwada, wadanda suka hada da na kan tudu, da bakin zuwa sama, da na kan ruwa da kuma kasan ruwa wadanda duk ba’a dade da shigar da su cikin makaman da ake aiki da suba.
Tun kafin yakin kwanaki 12 ne rabuwar kasar da yin atisayen soje. Na karshe da suka yin a hadin giwa na tsare da kasashen Rasha da China. Ana gudanar da atisayen ne a arewacin tekun Indiya da kuma tekun Omman.