Sojojin Najeriya: ‘Yan Ta’addan Boko Haram Na Samun Kudi Ne Daga Kasashen Ketare

Najeriya ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki hanyoyin samun horo da kudade ’yan ta’addan Boko Haram da suka shafe shekara 16 suna addabar

Najeriya ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki hanyoyin samun horo da kudade ’yan ta’addan Boko Haram da suka shafe shekara 16 suna addabar kasar.

Babban Hafsan Tsaro Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya yi wannan kiran a wata hira da kafar yada labarai ta Aljazeera ta yi da shi kan matsalar tsaro a ƙasar.

Janar Christopher Musa ya wanda ya dora ayar tambaya kan yadda ayyukan suka ci gaba a tsawon shekara 16 duk da yadda sojoji ragargajarnsu, ya yi zargin makarkashiyar kasashen duniya wajen sama wa kungiyar kudade da horo da kuma makamai.

Ya ce aka akasarin mayaƙan Boko Haram da sojoji ke kamawa ana samun su dauke da kudade  manyan kasashen duniya, wanda hakan ke nuna alamar kasashen duniya na da hannu wajen kulla makarkashiya da ayyukan kungiyar.

Ya kuma buƙaci Majalisar ta yi bincike kan sabuwar dabarar da ƙungiyar ta ɓullo da ita ta amfani da jirage marasa matuƙa wajen yin leƙen asiri karin su kai wa jami’an tsaro hari.

Da yake amsa tambaya kan dalilin da mayakan Boko Haram ke sake taruwa su kai hare-hare bayan sojoji sun yi iƙirarin murƙushe su, Janar Christopher Mustapha, ya ce ya yi zargin akwai kudade  da kasashen duniya ke ba wa ’yan ta’addar, yana mai neman Majalisar Dinkin Duniya ta shigo domin gano masu hannu a daukar nauyin ’yan ta’addan.

Sai dai ya bayyana cewa ba shi da masaniyar kasashen da ke neman hana Najeriya zama lafiya, duk da cewa ba ita ce kaɗai kasar da ke fama da ’yan tayar da kayar baya ba, a yankin Sahel da ma Afirka ta Yamma ana fama da irin wannan matsala.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments