A wata wasika wacce tsoffin sojojin Najeriya 38 suka rubutawa ministan sharia kuma Antony Janar na kasa, Lateef Fagbemi, tsoffin sojojin wadanda rundunar sojojin kasar ta kora daga ayyukansu a shekara ta 2016, sun bukaci Antony Janar din ya dubi al-amarinsu ya kuma maidasu kan ayukansu, tare da biyansu hakkokinsu.
Jaridar Premium time ta Najeriya ta bayyana cewa. Danladi Hassan mai mukamin Kanar da wasu abokan aikinsa 37 sun ce rundunar sojojin kasar ta koresu daga ayyukansu a shekara ta 2016 ba tare da gabatar da su a gaban kotun soje wacce take da hurumin yin haka ba.
Labarin ya kara da cewa rundunar ta kori sojojin 38 ne bayan zarginsu da aikata almundahana. Kuma sun ji labarin korarsu ne a gidan radiyo, ba tare da an basu wata takarda wacce take masu bayanin irin laifukan da suka aikata ba.
Wasikar wacce sanannen lauya nan, Falana and Falana’s Chambers, ya rubuta ta bukaci Ministan sharia kuma Antony Janar na kasa ya sake duba al-amarinsu, ya kuma maida su kan ayyukansu.
Jaridar Premium time ta gano cewa daya daga cikin sojojin da aka koran, mai suna Baba Ochankpa ya rasu a shekara ta 2017.