Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Hadu Da Fushin ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar

‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan

Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka kaddamar da munanan hare-hare a kan sansanin Jenin sannan wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi luguden bama-bamai kan gidajen Falasdinawa. A gefe guda kuma, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun gudanar da arangamar da sojojin mamayar, a sansanin Askar da ke gabashin Nablus. Yayin da a birnin Nablus aka yi artabu mai tsanani tsakanin ‘yan gwagwarmayar na Falasdinu da sojojin mamayar Isra’ila.

A halin da ake ciki kuma, Bataliyar Nablus da ke karkashin Sarayal-Quds na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da kai wa sojojin mamayar Isra’ila hari da harsasai da tada bama-bamai, yayin da dakarun shahidan Al-Aqsa suka tabbatar da gwabza kazamin fada da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments