Ma’aikatar kiwon lafiya ta yankin Gaza ta sanar da cewa, sojojin mamaya sun kama manajan asibitocin tafi-da-gidanka Dr. Marwan al-Hums a lokacin da ya kai ziyarar aiki a wani budadden asibiti na “Red-Cross” a yammacin Khan-Yunus.
Jami’i a ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza Dr. Munir al-Barsh ya bayyana cewa; Sojojin HKI su ka kama al-Hums, kuma sun jikkata daya daga cikin wadanda suke a tare da shi, yayin da wasu ‘yan jarida biyu su ka yi shahada da suke a kusa da wurin da aka kama shi.
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta dora alhakin kare lafiyar Dr. al-Hums akan wuyan HKI, tare da yin ishara da cewa kamun yana a karkashin ci gaba da kai wa ma’aiktan kiwon lafiya hare-hare,tare da cewa, ya zuwa yanzu ‘yan sahayoniyar sun kama ma’aikatan kiwon lafiya 360 da kuma kashe wasu 1,589.
Shi kuwa manajan Asibitin “Majma’a-Shifa” Dr. Muhamamd Abu Salmiyyah, ya fada wa tashar talabijin din aljazira cewa; ya kamaya kungiyoyin kasa da kasa su yi matsin lamba da a gano inda Dr. Marwan al-Hums yake.
Dama dai tun a ranar 27 ga watan Disamba 2024 sojojin HKI su ka kama Dr.Husam Abu Safiyyah wanda shi ne babban likitan Kamal Adwan dake arewacin Gaza. A halin da ake ciki yana fama da cutuka da su ka sa nauyinsa ya ragu da kilo 40.