Sojojin Kasar Siriya Sun Girka Rundunoninsu A Kan Iyakar Kasar Da Kasar Iraki

A karon farko tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-asad na kasar Siriya, sabuwar gwamnatinn kasar ta aika sojoji tare da wasu dauke da makamai zuwa

A karon farko tun bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-asad na kasar Siriya, sabuwar gwamnatinn kasar ta aika sojoji tare da wasu dauke da makamai zuwa kan iyakar kasar da Kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto tashar talabijin ta ‘Iraqiyya’ ta kasar Iran na cewa a karon farko an ga sojojin kasar Siriya sanya da jajayen hula tare da wasu dauke da makamai wadanda jimillarsu ya kai 200, sun zo sun tsaya a kofar shiga kasashen biyu da ke Bukamal.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Iraki ta jibge dubban jami’an tsaro a kan iyakokin kasashen biyu, bayan faduwar gwamnatin Asad, don tabbatar da cewa yan ta’adda musamman na Daesh basu ratsa sun shigo kasar ba.

Labarin ya kara da cewa kasashen Iraki da siriya suna da iyaka wanda ya kai tsawon kilomitan  620.

Banda haka labarin ya bayyana cewa motoci da mutane suna kai kawo a tsakanin kasashen biyu. Wasu yan iraki sukan shiga kasar Iraka daga kofar, sannan yan siriya da dama sun tsallak zuwa kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments