Search
Close this search box.

Sojojin Kasar Iran Sun Zama Abin Alfahiri Da Kuma Dogora Ga Mutanen Kasar

A hudubobinsa na sallar Jumma’a a jiya, a nan Tehran, Ayatullah Ahmad Khatami ya bayana cewa sojojin kasar sun zama abin alfahari sannan abin dogaro

A hudubobinsa na sallar Jumma’a a jiya, a nan Tehran, Ayatullah Ahmad Khatami ya bayana cewa sojojin kasar sun zama abin alfahari sannan abin dogaro don kare kasar daga makiya da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto limamin yana cewa maida martini wanda sojojin kasar suka yi kan HKI a cikin kwanakin da suka gaba ta, gargadi ne kawai, amma idan ta sake yin wani kuskure irin wannan za ta gamu da fushin sojojin kasar fiye da ta ranar 14 ga watan Afrilun da muke ciki.

A hare haren maida martanin JMI na ranar 14 ga watan Afrilu dai HKI ta fahimci cewa JMI ta Iran da gaske take a duk abinda ta sa a gaba musamman wanda ya shafi tsaron kasar.

A ranar 14 ga watan Afrilun da muke ciki ne sojojin Iran tare da dakarun kare juyin juya halin musulunci a kasar Iran su ka harba akamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki na  kunan bakin wake fiye da 300 a kan cibiyoyin tsaro na HKI, inda da dama daga cikin makamaan saun isa inda aka harba su, sun kuma yi barna mai yawa  ga HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments