Manya manyan Jami’an sojojin kasar Iran sun musanta zantuttukan da ke yawo da su dangane da hatsarin jirgin shugaban kasa Syyid Ibrahim ra’isi wanda ya yi sanadiyyar shahadarsa da wasu jami’an gwamnatin kasar.
A shekarar da ta gabaya ce, jirgin shugaban kasa tare da ministan harkokin wajen kasar yayi hatsari a kan tsaunukan azarbaija na yamma.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an sojojin kasar na cewa, a iya bicikensu rashin kyawun yanayi ne ya haddasa fadauwar jirgin shugaban kasar ba wanu abu dabam ba.
Sojojin sun musanta ce wa, matsalar inji, ko bom, makamin makiya, ayyukan ta’addanci basu haddasa hatsarin jirgin shugaban kasar ba kamar yadda wasu suke yadawa.
Kafin haka dai wani tsohun dogarin shugaban ya bayyana cewa an gargadi shugaban kan kada ya je kasar ta Azerbaijan a lokacin.
Banda haka wani dan majalisar dokokin kasar ya bayyana a cikin majalisa kan cewa akwai abubuwan da basu bayyana ba dangane da mutuwar shugaba Ra’isi.