A jiya Laraba sojojin mamayar HKI sun keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a kuancin Lebanon inda su ka kama mutane 4 bisa riya cewa sun karaci inda suke.
A wata sanarwa da sojojin na mamaya su ka fitar sun ce sun kama mutane 4 ne saboda sun karaci inda suke.
A gefe daya, sojojin kasar Lebanon sun yi kira ga ‘yan kasar da suke komawa gidajensu, da su kaucewa isa wuraren da sojojin mamaya suke.
Sanarwar da sojojin kasar ta Lebanon su ka fitar ta kunshi cewa; Muna yin kira ga ‘yan kasa da suke kowama zuwa garuruwan da suke kan iyaka, musamman yankunan Sur, Bint-Jubail da Marjiiyyun, da su kaucewa karatar inda sojojin mamaya suke.”
Sojojin na kasar Lebanon sun cigaba da cewa, manufar wannan kiran shi ne kare lafiyar ‘yan kasa saboda kar ‘yan mamaya su kai musu hari.
Kasa da sa’a daya daga tsagaita wutar yaki da misalin karfe; 4;00 na dare a Lebanon, mutanen kudancin Lebanon da su ka zama ‘yan hijira, su ka fara komawa garuruwansu.