Sojojin HKI Sun Kara Zafafa Hare-Hare A Arewacin Gaza. Sannan Sojojin Kasa A Arewa Da Kuma Kudancin Yankin Suna Kara Kutsawa Cikin Yankin

Akalla mutane 47 ne sojojin HKI suka kashe ko kuma suka yi shahada a cikin yan sa’oin da suka gabata a arewacin zirin Gaza. Kamfanin

Akalla mutane 47 ne sojojin HKI suka kashe ko kuma suka yi shahada a cikin yan sa’oin da suka gabata a arewacin zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin yahudawa sun kara zafafa hare-hare a kan arewacin zirin Gaza a cikin sa’o’in da suka gabata inda suka kashe akalla Falasdinawa 47.

Labarin ya kara da cewa, da misalin karfe 4 na safiyar yau jumma’a ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan arewacin Gaza inda mutane 5 suka yi shahada nan take a tsakiyar garin. Sannan a sansanin yan gudun hijira na Nusairat kuma, sojojin yahudawa sun kashe falasdinawa akalla 27.

Har’ila yau sojojin yahudawan sun kara yawan sojojinsu na kasa a arewa da kuma kudancin zirin Gaza.

Majiyar asbitin Al-Awda da ke tsakiyar Gaza, ta bayyana cewa ta karbi gawakin Falasdinawa 16 da kuma wasu mutane 55 na wadanda suka ji rauni. Banda haka a Beit Lahiya kuma mutane 4 ne suka yi shahada, sannan mutane 2 sun yi shahada a mashigar asbitin Kamal Adwan sanadiyyar boma-boman jiragen yakin HKI. Sai kuma a Jabalia, akalla mutum guda ne ya yi shahada

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments