A cigaba da aikata laifukan yaki da sojojin HKI suke yi, sun kai wa sansanin ‘yan hijira na Falasdinawa na Deir Balah hari wanda ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkata Falasdinawa da dama.
Tashar talabijin din ‘ Palastine Today’ ta bayar da labarin da yake cewa; Falasdinawa da dama ne su ka yi shahada da kuma jikkata.
Bugu da kari rahoton tashar talabijin din ta “Palastine Today” ya kuma ce; A harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa hemomin ‘yan hijira dake kusa da asibitin Shuhada’ul-Aqsa, akalla Falasdinawa 4 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 21 su ka jikkata.
Daga cikin wadanda su ka jikkata da akwai ‘yan jarida da dama. Daga bude yaki akan Gaza da ‘yan sahayoniyar su ka yi, sun kashe ‘yan jaridar da adadinsu yah aura 130, Falasdinawa da kuma ‘yan kasashen waje.
Gwamnatin kwarya-kwarya ta Falasdinu ta fitar da bayanin yin Allawadai da wannan laifin yakin na baya da HKI ta tafka na kai wa hemomin ‘yan hijira hari.