Search
Close this search box.

Sojojin HKI 155 Ne Mayaka Falasdinawa Suka Halaka A Yakin Gaza Inda Suke Fafatawa Da Juna

Wani kwamandan daya daga cikin rundunonin sojojin HKI a Gaza, ya bada sanarwan halakar sojojin rundunarsa 155 a fafatawa da dakarun falasdinawa. Kamfanin dillancin labaran

Wani kwamandan daya daga cikin rundunonin sojojin HKI a Gaza, ya bada sanarwan halakar sojojin rundunarsa 155 a fafatawa da dakarun falasdinawa.

Kamfanin dillancin labaran Meher na kasar Iran, ya bayyana cewa banda sojojin da suka halaka, dakarun Falasdinawa sun kama wasu sojoji 9 da ransu,  sun kuma tafi da su.

Amma a wani labarin da kafafen yada labaran HKI suka watsa, sun tabbatar da halakar soja guda a garin Rafah na yankin Zirin Gaza. Har’ila dakarun Izzuddeem Kassam reshen soje na kungiyar Hamas,  ya bayyana cewa mayakansa sun sami nasara wargaza wata cibiyar kula da hare -haren sojojin HKI a Gaza, wanda ake kira ‘Natzarim, tare da amfani da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa.

Gwamnatin HKI dai tana buye adadin sojojinta da aka halaka a yakin da ke faruwa a Gaza, saboda tsoron rikicin cikin gida, idan yahudawan sun san da babarin.

Kan kowa ya san cewa adadin wadanda aka kashe a cikin sojojin HKI, wanda hukumomin kasar suke bayarwa ya bambanta da na wanda asbitocin kasar suke bayarwa nesa ba kusa ba.

Da wannan dalilin ne tashar talabijin ta 12 ta HKI ta bada labarin cewa gwamnatin kasar ta umurci shuwagabannin asbitocin kasar su dakatar da bada lissafi ko adadin wadanda suka halaka ko suka jinya a cikin sojojin kasar a asbitocinsu, sai bayan sun sami izini da sojojin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments