Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hari Kan Birnin Beirut Na Kasar Lebanon

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wani sabon hari kan birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon Jiragen saman yakin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila

Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wani sabon hari kan birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon

Jiragen saman yakin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da wani sabon farmaki kan yankin Zoqaq al-Blat da ke birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.

Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Jama’a ta kasar Lebanon ta fitar da sanarwa cewa: Farmakin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan yankin Zoqaq al-Blat a birnin Beirut ya yi sanadin shahadan mutane 5 tare da jikkatar wasu 24 na daban.

Kafofin yada labaran kasar Labanon sun rawaito cewa: An kai harin ne a kusa da Husainiyyar al-Zahra da ke yankin na Zoqaq, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane, kamar yadda bayanan farko suka nuna.

Rahotonni sun bayyana cewa: An kaddamar da farmakin ne a kan Zoqaq al-Blat da makamai masu linzami guda biyu, kuma motocin daukar marasa lafiya sun yi ta zirga-zirga a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments