Sojin Iran Sun Ce Suna Cikin Shiri Fiye Da Ko Wane Lokaci

Dakarun Jamhuriyar Musulunci sun fi karfi fiye da yadda suke a farkon yakin.

Sojojin Jamhuriyar Musulinci Ta Iran, sun bayyana cewa suna cikin shiri fiye da ko wane lokaci akan duk wata barazanar fuskantar hari daga makiya.

Birgediya Janar Mohammad Akraminia, kakakin rundunar sojan Iran, ya bayyana cewa a yau, dakarun kasar sun fi karfi, sun fi gogewa, kuma sun fi kasancewa cikin shiri sosai idan aka kwatanta da farkon yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan kasar.

Janar Akraminia ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron tunawa da shahidai a birnin Pishva a daren Juma’a, inda ya jaddada cewa rundunar soji, da Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), da kuma ‘yan sanda, sun kara samun kwarin gwiwa bayan watanni na fafatawa mai zafi.

“Dakarun Jamhuriyar Musulunci sun fi karfi fiye da yadda suke a farkon yakin, saboda gogewar da aka samu wajen fuskantar Amurka da kuma gwamnatin sahyoniyawa, in ji shi.

Ya kuma ba wa jama’a tabbacin cewa sojojin kasar suna shirye tsaf don kare kasar, tare da ingantattun kayan aiki da dabarun yaki.

Kakakin rundunar sojin ya yi nuni da cewa Iran tana da cikakken iko na dabarun yaki a kan Mashigar Hormuz.

Ya bayyana cewa kafin yakin, matsakaicin adadin jiragen ruwa 130 ne ke wucewa ta wannan hanyar a kowace rana, inda suke dauke da kusan kashi 20 cikin dari na man fetur na duniya, tare da man jiragen sama da takin zamani na sinadarai.

“Amma yanzu wannan duk iko yana hannun Iran, kuma har sai an amince da sharuddan da Jamhuriyar Musulunci, kafin a sake bude Mashigar Hormuz ba,” in ji shi.

Janar Akraminia ya kuma yi gargadi game da yiwuwar sake farmawa Iran da yaki daga bangaren Amurka.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted