Shugabannin kasashen Iran da Rasha sun bayyana cewa; Kulla yarjejeniyar dabarun ita ce ginshikin fadada alakar hadin gwiwa tsakaninsu
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada wajabcin zurfafa da karfafa alakar da ke tsakanin kasashen da suke ‘yan uwan juna kuma abokai irin Rasha.
Masoud Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, inda ya ce, “Kafin tafiyar tasa ya ziyarci Jagoran juyin juya halin Musulunci, inda Jagoran ya jaddada karfafa alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Rasha da suke ‘yan uwan juna kuma abokai zuwa mataki mai girma.
Ya kara da cewa: “Abin sa’a, sadarwar tsakanin bangarorin biyu tana kara kyautatuwa a kowace rana, kuma harkokin kasuwanci, al’adu da tattalin arziki suna ci gaba habaka da bunkasa.
Shugaban na Iran ya ce: “Sun shafe shekaru da dama suna aiki don shirya wani cikakken shiri na tsare-tsare, kuma a yau ne za a rattaba hannu kan wadannan takardu, kuma sun samu damar zurfafa tuntubar junansu a dukkanin bangarorin tsaro, tattalin arziki, kasuwanci da al’adu.”