Shugaban Senegal Ya Sanar Da Kawo Karshen Kasantuwar Dukkan Sojojin Ketare A Kasar

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar cewa, “za’a kawo karshen kasantuwar dukkan sojojin kasashen waje a kasar daga shekarar nan ta 2025 da

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar cewa, “za’a kawo karshen kasantuwar dukkan sojojin kasashen waje a kasar daga shekarar nan ta 2025 da aka shiga a yau.

Shugaba Bassirou ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar na  sabuwar shekarar.

Dama a ranar 28 ga Nuwamba, ya ba da sanarwar cewa dole ne Faransa ta rufe sansanonin sojinta a Senegal.

Yanzu ya tabbatar da cewa za a yi hakan ne a farkon shekara ta 2025.

Shugaban kasar Senegal ya bayyana cewa, “Na umurci ministan sojojin kasar da ya gabatar da wani tsari na hadin gwiwa a harkokin tsaro da ya shafi kawo karshen zaman sojojin kasashen ketare a Senegal daga shekarar 2025.

Ya ce “Dukkan kawayen kasarsa za a dauke su a matsayin abokan hulda, a cikin tsarin hadin gwiwa.

A watan Afrilu ne Bassirou Faye, Ya hau karagar mulki a kasar ta Senegal bisa taken alkawarin samun mulki da kuma kawo karshen dogaro da kasashen ketare.

Matakin raba gari da sojojin kasashen ketare na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummun kasashen Afrika da dama ke bukatar ficewar sojojin musamman na faransa, bayan da hakan ta wakana a kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Nijar, sai kuma Chadi a baya baya nan wace ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da kasar faransa a yankin Sahel.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments