Shugaban Ofishin Siyasar Kungiyar Hamas Ya Ce: Birnin Qudus Shi Ne Zai Zama Tushen Rikici

Shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Tururruwar yahudawan sahayoniyya zuwa birnin Qudus yana tabbatar da cewa Qudus ne tushen rikicin Falasdinu Shugaban ofishin

Shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Tururruwar yahudawan sahayoniyya zuwa birnin Qudus yana tabbatar da cewa Qudus ne tushen rikicin Falasdinu

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Ismail Haniyeh, ya bayyana cewa: Tururruwar tsagerun yahudawan sahayoniyya zuwa birnin Qudus lamari ne da ke tabbatar da cewa; Qudus ne tushen rikicin da za a yi fama da shi tsakanin Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya, yana mai jaddada cewa: Al’ummar Falastinu ba za su gajiya ba har sai sun kori ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya tare da kafa kasar Falasdinu mai cin cikakken gashin kanta kuma Qudus a matsayin babban birninta.

Haniyeh ya kara da cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa za su yi aiki da gaske da gaskiya kan duk wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta a yakin da ake yi a Gaza, da jaddada wajabcin ficewa gaba dayan sojojin mamaya daga yankunan Zirin Gaza, da kuma cimma matsaya kan musayar fursunoni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments