Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa

Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa

Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa

Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu.

Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka na neman korar Falasdinawa da suke zaune a Zirin Gaza zuwa hijira da nufin kwace musu kasarsu ta hanyar dabarar siyasa.

A wani labarin kuma, majiyoyin Masar da suke Amurka sun bayyana cewa: Ma’aikatar tsaron Amurka ta “Pentagon” ta shiga cikin jerin masu  barazanar ga Masar matukar ta ki amincewa da shawarar Trump na neman korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, wanda ke nufin kwace wa Falasdinawa kasarsu, kamar yadda shafin yanar gizon Al-Araby Al-Jadeed ya bayyana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments