Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran

A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar fari a yankunan da aka mamaye na Falasdinu, ya bayyana cewa; ‘Yan Nazi na karni na 21, wadanda suka kai hari kan babbar tashar ruwa da ke arewacin birnin Tehran a dandalin Tajrish da makami mai linzami, a yanzu haka suna kokarin yaudarar al’ummar Iran da kofin ruwa da aka yi masa magani. Amma al’ummar Iran a tsawon tarihi, sun dauki ko da mafi gogaggen su a matsayin ba komai ba ne, sun jefa su cikin kwandon shara.

Mohammad Baqir Qalibaf ya wallafa wani sako a shafin sada zumunta na “X” a yammacin jiya Laraba, inda ya ce: ‘Yan Nazi na karni na 21 sun kai hari kan babbar tashar ruwa ta birnin Tehran a dandalin Tajrish da rana tsaka don hana Tehran ruwa. Haka nan a Falasdiu da Gaza, wadannan mayagun halitta suke sace Ruwan duniya tun tsawon lokaci,    suna kokarin mayar da kishin ruwa a matsayin makamin yakaer Falasdinawa kamar yadda mafi yawan kungiyoyin kasa da kasa suka tabatar.”

Ya kara da cewa: “Karancin albarkatun ruwa a ‘yan shekarun nan ya sa wasu kauyukan yankunan da aka mamaye suna samun ruwa na sa’o’i 12 kacal a duk mako. A bana, dubban kadada na gonaki da gonakin noma a yankunan da aka mamaye sun bushe, kamar yadda wasu koguna suka kafe. Kungiyar manoma ta Isra’ila tana sa ran samun raguwar kayayyakin noma a wasu gonakin noma, saboda karancin ruwa da rashin biyan diyya”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted