Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya gargadi kasashen da suke makwabtaka da Siriya da kada su fada cikin tarkon ‘yan sahayoniyya da Amurka
Kakakin majalisar shawarar Musulunci ta Iran Mohammad Baqir Qalibaf, ta hanyar wani sako, ya gargadi kasashen da suke makwabtaka da Siriya game da fadawa cikin tarkon Amurka da na ‘yan sahayoniyya, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan gwagwarmayar Siriya wajen fuskantar ta’addanci.
Kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i yayin da yake yin tsokaci kan al’amuran da suka faru a cikin kwanaki biyun da suka gabata a kasar Siriya, ya yi gargadin dawowar kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi a kasar Siriya, yana mai kira da a dauki kwararan matakai tare da kwakkwaran hadin kai domin dakile sake yaduwar ta’addanci a yankin Gabas ta Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya yi kakkausar suka kan duk wani nau’in bayyanar ta’addanci, yana la’akari da yunkurin kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya a cikin ‘yan kwanakin nan da suka gabata a matsayin wani mummunan shiri na ‘yan ta’addan yahudawan sahayoniyya da Amurka da ke nufin dagula harkokin tsaro a yankin yammacin Asiya. Yana mai jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan da samun hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin, musamman wadanda suke makwabta da kasar Siriya, da su shirya daukan matakan dakile wannan makarkashiya mai hatsarin gaske.