Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya gana da tawagar ‘yan Majalisun kasar Habasha
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya gudanar da zaman tattaunawa da Sheikh Ibrahim Tufa, shugaban majalisar dokokin kasar Habasha.
Shugaban Majalisar shawarar Musulunci, ya gana da Sheikh Ibrahim Tofa, shugaban majalisar koli ta kasar Habasha, inda suka tattauna kan muhimmancin hadin kai a tsakanin mazhabobin addinin Musulunci.
A wannan zaman taron, shugaban majalisar shawarar Musuluncin ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin mazhabobin Musulunci inda ya bayyana cewa: Akwai addinai daban-daban a kasar Iran, kuma a majalisar shawarar Musulunci akwai wakilan Shi’a da Sunna da kuma na sauran mabiya addinai kamar Kirista, Yahudawa da Zortash.