Shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro ya kara jaddada matsayinsa na goyon baya ga gwagwarmayar Falasdinawa, kuma ya kirashi da, “tafarki mafi gaskiya da na taba sani a wannan lokaci”.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Madoro yana fadar haka a taron goyon bayan al-ummar Falasdinu ta kasa da kasa wanda aka gudanar a kasar a jiya Jumma’a 29 ga watan Nuwamba na shekara ta 2024.
Madoro ya kara da cewa, a cikin shekaru 100 da suka gabata babu wata gwagwarmaya ta neman yenci da adalci a duniya, wacce tafi gwagwarmayan Falasdinawa ta neman dawoda kasarsu da aka mamaye.
A shekara ta 1977 ne babban zauren MDD ya zabi ranar 29 ga watan Nuwamba na ko wace shekara a matsayin ranar goyon bayan Falasdinawa ta duniya. A irin ranar ce, a shekara 1947 aka gabatar da kudurin raba kasar Falasdinu tsakanin Falasdinawa da yahudawan Sahyoniyya a MDD.
Shugaban ya kara da cewa gwagwarmayan Falasdinawa, gwagwarmaya ce wacce ta hada kan dukkan mutane a duniya kan cancantarta, da kuma dacewarta.
Daga karshe shugaban kasar Venezuela ya ce gwamnatin kasarsa zata ci gaba da goyon bayan gwagwarmayan Falasdinawa, har zuwa ranar da zamu hadu a birnin Qudus a matsayin masu samun nasara a kan yahudawan Sahyoniya da masu goyon bayansu.