Shugaban Kasar Venezuela Ya Nuna Cikakken Goyon Bayansa Ga Gwamnatin Syria

Shugaba Nicolas Maduro ya bayyana cikakken goyon bayan kasarsa Venezuela ga gwamnati da al’ummar Syria da suka fada da ta’addanci da ‘yan ta’adda da kuma

Shugaba Nicolas Maduro ya bayyana cikakken goyon bayan kasarsa Venezuela ga gwamnati da al’ummar Syria da suka fada da ta’addanci da ‘yan ta’adda da kuma kasashen da suke goyon bayansu.

Shugaba Maduro  wanda ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Syria Basshar Asad ya  bayyana masa cewa: “Abinda  kasashen turai da Amurka suke son yi, shi ne raunana gwamnatin Syria saboda matsayin da take da shi a cikin wannan yankin da kuma cin gashin kanta.

A nashi gefen shugaban kasar Syria Basshar Asad ya jaddada cewa; Babu makawa ga kasashe masu cin gashin kansu, sai su fuskanci makirce-makircen yammacin turai da kuma Amurka, haka nan kuma fada da ta’addanci da kuma samun galaba a kansa.

Shugaba Basshar Asad ya bayyana cewa ta’addanci yana daga cikin makirce-makircen kasashen turai da Amurka akan kasashe masu cin gashin kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments