Shugaban Kasar Iran Yace Hadin Kan Musulmi Shi Ne Mataki Na Farko Na Ganin Bayan HKI A Yankin Asiya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce samar da hadin kai mai kwari a tsakanin tsakanin musulmi shi ne kawai zai bada damar fuskantar ayyukan

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce samar da hadin kai mai kwari a tsakanin tsakanin musulmi shi ne kawai zai bada damar fuskantar ayyukan ta’addancin HKI a yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Laraba a lokacinda yake ganawa da tokwaransa na kasar Iraki Abdul Latif Rashid a birnin Bagdaza babban birin Iraki inda yake ziyarar aiki na kwanaki uku.

Shugaban ya bukaci a dauke iyakoki da ke tsakanin kasashen musulmi wanda wani mataki ne na hada kan kasashen musulmi, kamar yadda kasashen turai suka zama kusan kasa guda saboda dauke kan iyakoki ga mutanen kasashen yankin.

Paezeshkiyan ya kara da cewa hadin kan al-ummar musulmi ko kasashen musulmi shi ne mataki na farko na kawarda HKI a tsakanin kasashen yankin.

Shugaban ya bukaci a kara dankon zumunci tsakanin kasashen Iran da Iraki a bangarori daban daban. Sannan daga karshe ya bukaci kasashen yankin Asia ta kudu su hada kai don  kula da al-amuran tsaron kasashensu, kada su dogara da wasu don yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments