Shugaban Kasar Iran Ya Taya Falasdinawa Murnan Nasaral Da Suka Samu Kan HKI

Shugaban kasar Iran Masoud Pejashkiyan ya gabatar da jindadinsa, ga mutanen mutanen Palasdinu yana kuma jinjina masu, kan nasarar da suka samu kan HKI, bayan

Shugaban kasar Iran Masoud Pejashkiyan ya gabatar da jindadinsa, ga mutanen mutanen Palasdinu yana kuma jinjina masu, kan nasarar da suka samu kan HKI, bayan yarjeniyar tsagaita wutan da aka samu tsakaninsu da HKI.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da  cewa Palasdinawa a gaza sun nuna turjiya da kuma hakuri, na tsawon watanni 15 da suka gabata.

Shugaban y ace muna kara mika sakon murna ga mutanen gaza, da kuma Falasdinu gaba daya, kan wannan nasarar da suka samu a kan yahudawan,, duk tare da tallafi da suka samu daga Amurka da kuma kasashen yamma.

HKI bata cimma dukkan manufofinta da ta zayyana na fara yaki a gaza ba, wadanda suka hada da kwatar fursinoni yahudawan da Hamas take tsare da su a gaza. Shafe kubgiyar Hamas da kuma kwace Gaza gaba dayanta daga hannun Falasdiniwa, har ma su ginawa yahudawa gidaje a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments