Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Karfafa Samar Da Kayayyakin Bukatun Al’umma A Cikin Kasa

A jawabin da ya gabatar a gaban taron jama’ar birnin Mazandaran, Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya jaddada cewa: Suna da kwarewa a hare-haren

A jawabin da ya gabatar a gaban taron jama’ar birnin Mazandaran, Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya jaddada cewa: Suna da kwarewa a hare-haren mayar da martani musamman wadanda suka kaddamar kan haramtacciyar kasar Isra’ila na “Alkawarin Gaskiya’ wanda martanin an aiwatar da shi ne da taimakon dukkanin bangarori, da haka ya kara tabbatar da karfin Iran. Yana mai nuni da cewa, akwai yiwuwar gudanar da hadin kai da taimakekkeniya da kuma karfafa yarjejeniya tsakanin hukumomi da dakarun tsaro da masu fada a ji wajen iya cimma manyan ayyuka. Sayyid Ra’isi ya kara da cewa: Dole ne a kakkabe hannun masu banzantar da kayayyakin cikin gida da gudanar da almubazzaranci da dukiyar kasa, yana mai jaddada cewa, kada shigo da kayayyaki daga waje su yi illa ga abin da ake samarwa a cikin kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments