Search
Close this search box.

Shugaban Iran Ya Jaddada Hakkin Kasar Na Mayar Da Martani Kan Kisan Gillar Haniyya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A bisa dokokin kasa da kasa, Iran tana da ‘yancin mayar da martani kan duk wanda ya dauki matakin

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A bisa dokokin kasa da kasa, Iran tana da ‘yancin mayar da martani kan duk wanda ya dauki matakin wuce gona da iri kanta

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada matsayin Iran na kaucewa rikicin yaƙe-yaƙe da kuma habbasanta a fagen samar da zaman lafiya da tsaro a duniya. Yana mai ishara da kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suke yi wa mata da kananan yaran Falasdinawa, da kuma kisan gillar da suka yi wa bakon Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’il Haniyah, yana mai jaddada cewa hakan ya saba wa duk wani tushe tsarin dan Adamtaka dokoki, kuma Iran tana da hakkin mayar da martani a kan duk wanda ya dauki matakin wuce gona kan ta.

Wannan furuci na shugaban kasar ta Iran ya zo ne a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da ya gudanar da fira ministan gwamnatin Vatican, Bishop Pietro Parolin.

Kamar yadda Pezeshkian ya yaba da matsayin gwamnatin Vatican na goyon bayan zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro a matakin duniya, sannan daga karshe shugaban kasar ya yi kira ga gwamnatin ta Vatican kan matsayinta na karfafa rawar da take takawa tare da tuntubar kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da nufin hanzarta dakatar da ayyukan ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Zirin Gaza, da dage matakin killace yankin domin samun damar isar da taimakon jin kai ga al’ummar yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments