Shugaban kasar Iran Masoud Paezeshkiya ya halarci taron makokin 40 na shahidan ranakun 8 da 9 na watan Jenerun da ya gabata, wanda ya kai ga shahadar mutanen kasar kimani 2400.
Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban tare da samun rakiyar Jami’an gwamnatinsa sun halarci taron na 40 a hubbarin Imam Aliyu dan Musa Arridah (a) da ke birnin Mashad a arewa maso gabacin kasar.
A ranakun 8 da 9 na watan Jenerun da ya gabata ne gwamnatocin kasashen yamma musamman Amurka da HKI suka kaddamar da hare-hare tare da amfani da yan kungiyar yan ta’adda ta DAESH don kifar da gwamnatin kasar amma ba tare da samun nasara ba.
Sai dai hare-haren sun kai ga mutuwar mutane 3117, sannan sun lalata dukiyoyi na biliyoyin dalar Amurka.
An gudanar da tarurrukan 40 da shahadar wadannan mutanen Iran, ne a duk fadin kasar, don rokon Allah ta’ala ya jikansu ya kuma karbi shahadarsu ya kuma tadasu a ranar kiyama da Muhammad da Iyalan gidansa –amince Allah ya tabbatar da garesu- tsarkaka.