Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: An cimma yarjejeniya da kasashen turai dangane da yadda za’a yi watsi da batun sake dawo da takunkumi kan Iran, amma bangaren Amurka ya kawo cikas ga wannan yarjejeniya.
A lokacin da ya iso filin jirgin saman Mehrabad na Iran daga birnin New York, shugaba Pezeshkian ya yi tsokaci kan ganawarsa da wasu shugabannin kasashen Turai da suka yi da ba a taba gani ba, yana mai cewa, “A birnin New York, sun tattauna da Turawa kan batutuwan da suka jibanci lamarin makamashin nukiliyar Iran, kuma bisa ga dukkan alamu sun cimma matsaya.
Ya ci gaba da cewa: A zauren Majalisar Dinkin Duniya, sun gabatar da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa, musamman laifukan yahudawan sahayoniyya a Gaza.
Ya kara da cewa: Shahadar mutane sama da 65,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma killace mutanen Gaza, ba tare da samun ruwan sha, ko magunguna, ko agajin jin kai ba, wani bala’i ne na jin kai, amma abin bakin ciki shi ne shiru daga kasashen duniya.