Shugaban kasar Iran ya bukaci karfafa dangantaka tsakanin kasarsa da Azerbaijan

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana wajabcin bayar da fifiko kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran da Azarbaijan, yana mai cewa manufar Jamhuriyar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana wajabcin bayar da fifiko kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran da Azarbaijan, yana mai cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce ci gaba da karfafa alaka da makwabtanta.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da mataimakin firaministan kasar Azabaijan Shahin Mustafayev a babban birnin Tehran a wannan Talata.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da manufofin raya alaka da mu’amala da kasashe makwabta da na musulmi, kuma a wannan fanni dangantaka da kasar Azarbaijan tana da matukar muhimmanci a gare mu, in ji Pezeshkian.

Ya ci gaba da cewa, ci gaba da karfafa matsayin hadin gwiwa zai mayar da Iran da Azarbaijan manyan abokan hulda bisa manyan tsare-tsare. Shugaban na Iran ya buga misali da yarjejeniyoyin da aka cimmawa, da kuma ayyukan hadin gwiwa da ake gudanarwa a halin yanzu tsakanin kasashen biyu a fannin kasuwanci, makamashi da sufuri.

A nasa bangaren mataimakin Firaministan kasar Azarbaijan Mustafayev ya ce: A cikin shekaru da dama da suka gabata, Jamhuriyar Azarbaijan ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen fadada alaka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Bugu da kari, muhimman sauye-sauyen da muka gani a cikin wannan dan karamin lokaci na shugabancin ku, na nuni ne da samun makoma mai haske a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin.

Mustafayev ya kuma yaba da rawar da Iran ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, yana mai cewa Azarbaijan ta yi imanin cewa, “kasashen wannan yanki ne kadai za su iya warware matsalolin yankin da kansu, ba tare da yin katsalandan daga kasashen ketare ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments