Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Matsayin hikima na Yankin Kurdistan ya dakile makircin da ake yi a kan iyakokin yammacin Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana godiyarsa ga matsayin yankin Kurdistan mai tausayi da alhaki game da abubuwan da suka faru kwanan nan, yana mai cewa, “Masu kai hare-hare sun nemi raba Iran, amma al’ummar Iran sun kara zama masu hadin kai da fahimtar juna. Hikimar samun yankin Kurdistan ta dakile makircin da ake kullawa a kan iyakokin yammacin Iran.”
Fadar Shugaban kasar Iran ya ruwaito cewa: A lokacin ganawar Pezeshkian da Nechirvan Barzani, Shugaban yankin Kurdistan na Iraki, da tawagarsa da suka kawo Ziyara zuwa birninn Tehran fadar mulkin Iran don halartar juyayin bankwana na gawar Jagoran juyin juya halin Musulunci da ya shahada, Shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana godiyarsa ga kalaman tausayawa, goyon baya, da kuma matsayin gaskiya da abokantaka da yankin Kurdistan ya nuna wa al’ummar Iran. Ya kuma bayyana fatansa na karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu.
Ya yi nuni ga dadadden dangantakar tarihi tsakanin bangarorin biyu, yana mai cewa, “Iran, Iraki, da Yankin Kurdistan sun rayu tare tsawon ƙarnoni, waɗanda ke da alaƙa mai muhimmanci na tarihi, al’adu, zamantakewa, da iyali. Waɗannan abubuwa masu mahimmanci na iya zama ginshiƙi mai mahimmanci don kafa zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin gwiwa a yanki.”