Shugaban kasar Iran na riko, Mohammed Mokhber, ya jadadda ci gaba da fadada siyasar kasar da kasashen ketare .
A wata tattaunawa ta wayar tarho da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, Mohammed bin Salman, Mista Mokhber ya bayyana cewa, bunkasa alaka da kasashe makwabta da kawaye na daya daga cikin muhimman nasarori da dabarun Ayatullah Raisi, kuma shahadarsa ba za ta sauya tafarkin Iran ba.
Ya jaddada cewa, ci gaba da manufofin makwabtaka da bunkasuwar hulda da kasashen yankin na da matukar muhimmanci.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohamed Ben Salman.
Bin Salam, ya bayyana alhininsa game da rashin Ayatullah Raisi, shugaban kasar da ya yi shahada, ya kuma jaddada aniyarsa ta farfado da raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Ya bayyana cewa lamarin ya yi matukar zafi ga kasar Saudiyya, kuma rashin shugaba Raisi da ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian abun bacin rai.
Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da Tehran da Riyadh suke takawa a yankin da kuma duniyar musulmi, ya kuma jaddada cewa ta hanyar fadada alakarsu za su iya samar da makoma mai haske ga yankin.