Iran Ya Zargi IAEA Da Mika Kai Ga Amurka Da HKI

Shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Dr Mohammad Eslami ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA, saboda mika kai ga takurawar

Shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Dr Mohammad Eslami ya bayyana cewa hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA, saboda mika kai ga takurawar kasashen Amurka da HKI ta bar aikin da aka dora mata gada daya, ta koma kan abinda Amurka da HKI suke so.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar ya nakalto Islami yana fadara haka, a jiya Asabar a wani taro a nan Tehran dangane da hakan. Ya kuma kara da cewa fuska biyu wanda hukumar take nunawa ya zama aibi gareta, ya kuma maida ita kamar  kamfanin Amurka da HKI ne.

Islami ya ce, don fuska biyun  da hukumar take nuna wa ne, ya sa shuagban kasar Iran a jawabinsa a gaban shuwagabannin kasashe a babban zauren MDD karo 81 yake cewa makaman nukliya suna HKI amma masu bincike suna Tehran.

Islamu yace,  wannan hukumar wato IAEA wacce aka kafata  bayan yakin duniya na biyu, don hana yaduwar makaman nukliya a tsakanin kasashen duniya, da kuma kawo ci gaba na makamashin nukliya tsakanin kasashen duniya ba tare da bambanci ba a halin yanzu ta zama ma’aikata karkashin gwamnatin kasar Amurka.

Islami ya kammala da cewa IAEA ta kasa aiwatar da aikin da aka dora mata bayan kafatabayan yakin duniya na biyu musamman kan JMI.  A wani labarin kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Bakhaei ya bayyana cewa shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossi shi ne ya hadda yakin da Amurka da HKI suka kai wa kasar Iran. Baghaei ya bayyana haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa Grossi ya na amfani da hukumar IAEA don biyan bukatun yan siyasa. Amurka da HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted