Shugaban hukumar liken asiri ta kasar Amurka wato ” the US Central Intelligence Agency (CIA)” William Burns, ya tabbatar da cewa, ba wata shaida da suke da ta ita ta tabbatar da cewa shirin Nukliyar kasar Iran ta kera makaman Nukliya ne ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burns yana fadawa tashar radiyo ta (National Public Radio) NPR ta Amurka hakan.
Labarin ya nakalto Burns na fadar cewa, ai kasar Iran ta yi rauni sabuda abubuwan da suka faru ko suke faruwa a kudancin Asiya a baya bayan nan, sun kuma nuna cewa Iran ta yi rauni a cikin yan watanni 6 da suka gabata. Burns ya fada haka ba tare da gabatar da wani dalili ba.
Jami’in hukumar ta CIA ya kara da cewa, sabuda, abinda ya kira raunin da JMI tayi, gwamnatin Amurka mai kama aiki, tana iya amfani da wannan damar don tattaunawa mai zurfi da ita, idan ta ga dama.
Kafin haka dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh, na ma’aikatar harkokin wajen kasar ya sha nanata cewa shirin makamashin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, kuma shirin na tafiyar ne bisa yarjeniyar NPT, kuma hukumar IAEA tana sane da hakan.
Amma dangane da raunin JMI a cikin watanni 6 da suka gabata, kamar yadda Daraktan CIA ke magana, Janar Hussain Salami babban kwamnadan dakarun IRGC na JMI, ya karyata hakan ya kuma kara da cewa, Kasar Iran tana kara karfi ne, saboda dama bata dogara da kawayenta na kasashen wajen don kare kanta ba. Saboda hakane a lokacin gwamnatin Amurka ta Kashe Janar Qasim Sulaimani ta maida martani kan sansanin sojojin Amurka a kasar Iraki kai tsaye, ba tare da nemi wani taimaka daya waje ba.
Daga karshe yace, Janar Salami yace: Iran tana kula da mahsigar ruwa ta Hurmuz kamar yadda take a da, kuma tana tasiri a cikin harkokin siyasa da tattalin arziki a duniya, don haka ba abinda ta rasa.