Shugaba Pezeshkiya Yayi Watsi Da Shishigin Kasashen Waje A cikin Al-Amuran Kasarsa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya yi watshi da dukkan shishin da wasu kasashe suke yi a cikin al-amuran cikin gida na kasar, ya  kuma

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya yi watshi da dukkan shishin da wasu kasashe suke yi a cikin al-amuran cikin gida na kasar, ya  kuma bukaci a warware dukkan matsaloli a yankin yammacin Asia ta hanyar tattaunawa.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a a jiya Asabar a lokacinda yake jawabi a wani taron tattalin arziki, wanda ya maida hankali wajen zuba jari kan sifiri, wadanda suka hada da shimfida layin dogo da kuma gina hanyoyi.

A wani bangare na jawabinda shugaba Pezeshkiyan ya  bayyana cewa shuwagabannin kasashen yankin suna yin matukar kokari wajen ganin an rage matsaloli da tashe tashen hankula a yankin. Ya kuma kara da cewa, kasashen  Azerbaijan, Turkey, Iraq, Saudia, Masar , Qatar, UAE, Oman, Pakistan, Afghanistan da sauransu suna bukatar a warware matsalolin da ke faruwa a yankin ta hanyar tattaunawa da kuma zaman lafiya.

Y ace Iran tana gani kasashen yankin su zauna su tattauna a tsakaninsu don warware matsalolin yankin ba tare da shishigi daga wani daga waje ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted