Shugaba Pezeshkian ya jaddada wajabcin hadin kan al’ummar musulmi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira da a hada kai tsakanin al’ummar musulmi, yana mai cewa amfanin makiya yana cikin sabani tsakanin musulmi.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira da a hada kai tsakanin al’ummar musulmi, yana mai cewa amfanin makiya yana cikin sabani tsakanin musulmi.

Yace Idan musulmi suka hada kai, karfinmu na ci gaban tattalin arziki, kimiyya, da al’adu zai karu matuka kuma wannan ne ya sa makiyanmu ke kallon hadin kanmu a matsayin barazana,  kuma amfanin su yana cikin sabani da rarrabuwar kawunan musulmi inji Pezeshkian a wani taron manyan masana a birnin Basra, Iraki.

Don haka duk wani sako ko murya da ke haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmi sako ne na shaidan,” inji shi.

Pezeshkian wanda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a makwabciyar kasarsa a ranar Larabar da ta gabata ya ce “Dole ne mu hada karfi da karfe domin dawo da martabar musulmi a duniya.”

Yace “Idan da gaske mun  kasance a matsayin ‘yan’uwa, shin Isra’ila za ta iya kashe Musulmi a kowace rana gaza?” Ya yi wannan tambaya ne a lokacin da yek yin tsokaci kan kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza inda hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadin shahadar  Falasdinawa akalla 41,118 tare da jikkata wasu fiye da 95,000 tun daga watan Oktoban bara.

Ya ce Turawa sun yi ta gwabza fada da junansu sama da shekaru 100, amma a yau sun yi nasarar kawo karshen rikici da sabaninsu, sun hada hanyoyinsu, tare da kafa kudin bai daya tare da tabbatar da manufofinsu da suka hada su tare, in ji shi.

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da musulmi suke gudanar da bikin “Makon Hadin Kan Musulunci” a bana wanda ake yi a kowane lokaci na zagayowar Maulidin Manzon Allah, a daidai lokacin da Falasdinawa ke ci gaba da fuskantar mawuyacin hali a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments