Shugaba Pezeshkian Na Kasar Iran Yace: Zamu Ci Gaba Da Hanyar Shahid Kasim Sulaimani Da Karfi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa: zai bi sawun shahida Kasim Sulaimani saw da kafa da kuma dukkan karfimmu. Tashar talabijan ta Presstva

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa: zai bi sawun shahida Kasim Sulaimani saw da kafa da kuma dukkan karfimmu.

Tashar talabijan ta Presstva nan Tehran ta nakalto shugaban ya na fadar haka a taron tunawa da shahid Kasim Sulaimani shugaban rundunar Qudus karkashin dakarun kare juyin juya hali na musulunci a kasar Iran, wato IRGC, wanda shugaban Amurka na lokacin Donal Trump da kansa ya bada umurni ga sojojinsa su kashe shi a kasar Iraki, sun kuma aiwatar da kissan a rana irin ta yau 3 ga watan Decemban shekara ta 2020.

Kafin haka dai Shahida Janar Kasim sulaimani ya na daga cikin sojojin kasar Iran wadanda suka taimakamawa kasar Iraki da Siriya wajen samun nasarar a kan kungiuar yan ta’adda ta ISIS wacce ta kafa daula a kasashen Iraki da Siriya a tsakanin shekaru 2014-2017.

Kuma idan ba shahid Kasim da abokan aikinsa sun taimaka wajen murkushe daular kungiyar da Daesh ba, da sun tawatsa kasashen biyu.  

Wasu Jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa su suka kafa kungiyar Daesh don rarraba kasashen Iraki da Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments