Shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar bakin haure daga kasar ya fara lakume rayuka a jihar Mineapolis a jiya Laraba.
Tashar talabijan na Presstv a nan Tehran ya daruruwan jami’an shige da fice wadanda shugaban ya tura zuwa manya-manyan birane na kasar Amurka sun kashe wata mata a jihar Mineapolis da ke arewacin kasar. Shugaba Trump yak are Jami’in tsaron da yayi kissan kan cewa ya yi haka ne don kare kansa.
Labarin ya kara da cewa matan tana tuka mota a kokacinda jami’an shege da fice suka tunkareta, suka kuma bukaci ta tsaya. Wadanda suka sahidawa idanunsa sun bayyana cewa Jami’an shige da fishin ya yi harbi a kan matukin motan ne a dai dai lokacinsa ta tsaya ko kuma ta kusan tsayawa, kuma a nan take ta rasu.
Wani wanda ya ganewa idanunsa ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa, wani likita wanda yake wurin yayi kokari ya taimakawa matan amma jami’in tsaron ya auna bindiga a kansa tare da umurnin ya kauce. Ana cikin wannan halin jami’an kwana kwana suka zu suka tabbatar da mutuwarta.
Magajin garin Mineapolis dai ya bukaci jami’an tsaro shige da fice su bar jihar su kuma fice daga yanking aba daya.
Ba’a dade da kashe matar ba mutane suka yi gangami a inda abin ya faru suna zanga-zangar yin allawadai da samuwar wadan nan jami’an tsaro a jihar.