Sheikh Zakzaky:  Gwagwarmayar Musulunci A Lebanon Ta Sake Jaddada Kanta

Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane

Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane su ka halarci jana’izar yana nuni da cewa, gwgawarmayar musuluncin ta sake jaddada kanta.

Sheikh Ibrahim Yakub Ibrahim El_Zakzaky ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah yana a matsayin takaitaccen hoton al’ummar musulmi ne, kuma  gudanar da jana’izar da na gani yana nuni da cewa; Ruhinsa yana nan a raye cikin fagen daga.


Har ila yau jagoran ja harkar musulunci a Nigeria ya ce, abokan gaba ‘yan sahayoniya sun zaci cewa ta hanyar kisan gilla za su kawo karshen gwgawarmaya,amma abinda yake faruwa a yau, yana nuni da cewa gwgawarmaya ta kara sabunta kanta, kuma da yardar Allah wannan tafarkin zai kai ga samun nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments