Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Naem Qasim ya bayyana cewa kungiyar ta sami nasarar lalata shirin makiya don wargaza kungiyar duk tare da asarori masu yawa wanda kungiyar tayi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kungiyar ta Hizbullah yana fadar haka a wata wasika da ya rubutawa Ali-Akbar Vilayati daya daga cikin manya-manyan masu bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara.
Sheikh Qasim ya kara da cewa yakin da aka fafata tsakanin kungiyar da HKI na kwanaki 64 a shekara ta 2024 ya yi sanadiyyar shahadar wanda ya gada Sayyid Hassan Nasarallah, da Sayyid Hashin safiyuddeen da wasu kwamandojin kungiyar da dama. Yace yakin yayi tsanani amma kuma makiya sun kasa kaiwa ga manufofinsu na shafe kungiyar daga doron kasa.
Shugaban ya kara da cewa yayan kungiyar Hizbullah a shirye suke su ci gaba da biyayya da kuma bada shahidar a kan wannan tafarkin. Sheikh Qasim ya bayyana nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran a shekara ta 1979 a matsayin rahamar Allah da musulmi ga kuma duniya gaba daya. Ya ce nasarar ta farfado da addinin musulunci a gaban manya-manyan kasashen duniya a gabas da yamma da kuma goyon bayan al-ummar Falasdinu da aka zalunta.
Sheikh qasim ya jinjinawa JMI kan jajiircewa a gaban takunkuman tattalin arziki, na tsawon shekara 47 da suka gabata da yakin shekaru 8 da kasar Iraki, da yakin kwanaki 12 da wanda Amurka da HKI suka kaiwa kasar. Yace wannan juriyar da jajircewar suna tabbatar da cewa JMI da gaske take a kan tafarkin da ta dauka. Kuma yaba da sadaukarwan da dakarun IRGC suke yi a duk tsawon wannan lokaci. Daga karshe ya yabawa jagoran juyin juya halin musulunci a kekyawar jagorancinda da yake bawa kasar Iran da kuma musulmi a ko ina a duniya.