Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Naem Qaseem yace hare-haren da HKI ta kai kan kasar Qatar yana daga cikin shirinta na samar da ‘Isra’ila Babba’ Kuma gwamnatin kasar Amurka tana goyon bayan hakan.
Sheikh Naeem Qasem ya bayyana haka ne a yau Laraba a lokacinda yake jawabi ta kafar Bidiyo, dangane da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s) da kuma jikansa Imam jaafar Mohammad Assadik (a). Dangane da kasar Lebanon kuma,. Sheikh Qasim ya bayyana cewa, yana kira ga gwamnatocin yanking abas ta tsakiya su goyi bayan “Masu gwagwarmaya a yankin don su kadai ne zasu iya tunkarar HKI. Idan kuna son kare kasashen yankin ku goyi bayan kungiyar Hizbullah, don kowa ya san cewa kasar Lebanon tana daga cikin kasashe na farko-farko wanda HKI zata mamaye don cimma burinta na kafa Isra’ila babban, kuma kungiyar Hizbullah ce ta hanata samun hakan.
Daga karshen shugaban kungiyar ta Hizbullah ya bayyana cewa gwamnatin kasar Lebanon ta yi kuskure babba a ranar 5 da 7 ga watan Augustan da ya gabata, amma All…ya kiyaye sharrin wannan kuskuren, kuskuren haddasa yakin cikin gida wanda zai bawa HKI damar mamayar kasar Lebanon.